Wadanda aka nada shugabannin kwamitocin sun hada da wadanda suka yi adawa da Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar.
Sanata Saraki ya gargadi shugabannin da su tabbatar suna taro kodayaushe suna kuma sa ido akan bangarorin gwamnati da suka shafi ayyukansu saboda ciyar da kasar gaba. Yace sune zasu sa ido a madadin majalisar a bangaren zartaswa.Ya kira su hada kai domin su yi aiki tukuru.
A bangaren majalisar wakilai Husaini Suleiman Kangiwa yace korafe-korafen da ake yi basu da tushe saboda shugaban majalisa Yakubu Dogara ya yi adalci. Ya rungumi kowa. Ya ba kowa dama ya zabi kwamitin da yake so.
Wani abun da za'a lura dashi shi ne yadda Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar dattawa ya ba mutanen da suka yi adawa da zamansa shugaban majalisar shugabancin kwamitoci masu tasiri. Mutanen kuwa sun hada da Abdullahi Adamu shugaban kwamitin noma, George Akume shugaban kwamitin sojojin kasa, Danjuma Goje, kwamitin kasafin kudi, Ahmed Lawal kwamitin tsaro, Adamu Alero kwamitin kwastan da kuma Aliyu Wamako kwamitin ilimi.
To saidai Farfasa Yusuf Alhassan na Jami'ar Kansas ya yi fashin baki akan matakin da Sanata Bukola ya dauka dangane da ba wadanda suka yi adawa dashi kwamitoci masu tasiri.
Farfasa Alhassan yace Sanata Bukola ya yi hakan ne saboda ya jawosu kusa dashi ko a jikinsa domin ya samu biyan bukata a matsayinsa na sabon shugaban majalisar dattawa. Yace yakamata a lura cewa Sanata Saraki bashi da darajar shugabannin majalisar da suka shude. Lamarin ya yi kama da toshiyar baki.
Ga karin bayani.