Hukumar hana fasa kauri a Nigeria ta kona naman kajin turawa da aka shigo da shi ba bisa ka'ida ba. Hukumar ta kona ton dari da bakwai na naman kajin da aka shigo dasu a jihar Nija, arewa maso yammacin Nigeria.
Tuni dama gwamnatin Nigeria ta haramta shigowa da irin wannan naman kajin a kasar. Shugaban hukumar kwastan sashe na biyu dake da ofishi a Kaduna shine ya jagoranci kona naman kajin.
Ya shedawa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa gwamnati ta haramta a shigo dasu, a saboda dole aikin su ne su jawa wannan harka birki a saboda illar da yake yi. Ya kiyasta kudin naman kajin da aka kona zuwa naira miliyan daya da dari daya da ashirin da uku.
Yace bayanan sirri da uka samu a tsanin Jebbah da Mokwa ne ya taimakawa hukumarsa. Yace a jihar Kwara akwai kan iyaka, haka kuma a jihar Nija akwai kan iyaka.
Direban aka kama naman kajin a cikin motarsa mai suna Sirajo yace bai san ayi lodin kajin a cikin motar sa. A cewar sa lokacinda aka yi lodin motar baya wurin domin yana barci. Ya rantse da cewa in da ya gani da bai bari anyi lodin naman kajin a cikin motar sa ba.