Shirye-Shiryen Zaben 'Yan Nijar Mazauna Kasashen Waje

Mataimakin shugaban hukumar zabe ta kasa Dr Aladoua Amada

A yayin da kotun tsarin mulkin kasa ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana sunayen jam’iyu 10 da suka cancanci shiga zaben wakilan ‘yan kasar mazauna ketare a majalisar dokoki, hukumar zabe ta CENI ta dukufa kan ayukan isar da katuna da kayayyakin zabe zuwa kasashen da ya kamata a  gudanar da wannan zabe.

Mataimakin shugaban hukumar zabe ta kasar ta Jamhuriyar Nijar Dr. Aladoua Amada ya bayyanawa wakilinmu Souley Moumouni Barma a Yamai cewa "ba wata tantama ‘yan Nijer mazauna kasashen waje za su kada kuri’a a ranar 18 ga watan yunin 2023 kamar yadda aka tsara."

Saurari hirarsa da Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Akan Shirye Shiryen Zaben Yan Nijer Na Kasashen Waje