Da yake tsokaci kan wannan umarnin, Air Commodore Babagamawa mai ritaya, yace babu mamaki akwai hikima wajen sake bada wannan umarnin, domin hakan yana iya zaburadda dakarun su kara himma wajen ganin sun kamo Abubakar Shekau.
Gamawa, ya yaba da irin nasarori da sojojin suke kara samu kan 'yan ta'addan, ya bayyana fatar ganin an kawo karshen wannan ta'addanci baki daya ta ko wani fannin kasar.
Gameda tukuicin Naira milyan uku da rundunar sojojin ta ayyana ga duk wanda ya taimaka da bayanai da zasu ki ga kama Abubakar Shekau, yace a ganinsa sun wadatar, kuma wannan somin tabi ne.
Air Commodore Gamawa ya yaba da yadda gwamnati take kula da lafiya da jin dadin dakarun kasar.
Ga karin bayanin hirar da muka yi.
Your browser doesn’t support HTML5