Hayaniya ta Tashi a Zaman Farkon Majalisar Wakilan Najeriya

Ginin Majalisun Dokokin Najeriya

Bayan karshen hutun karewar shekara da 'yan majalisar wakilai suka je jiya sun yi zaman farko inda hayaniya ta tashi.
A majalisar wakilai an yi musayar yawu da tada jijiyoyin wuya yayin wata muhawara da ta yi tsanani.

Hayaniyar ta auku ne lokacin da shugaban marasa rinjaye Femi Gbajabiamila ya yi wasu kalamai na kankantaswar Leo Ogor wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar.

Abdullrahman Terab ya bayyana dalilan da ya sa aka samu hargitsin. A kasafin kudi da aka gabatar an yi shi ne tamkar har yanzu jam'iyyar APC ita ce marasa rinjaye wanda kuma a cewarsa ba haka bane. Dalili ke nan da Gbajabiamila ya yi kalamun da suka ta ma 'yan jam'iyyar PDP hankali. Ya ce a iyakar saninsa APC nada wakilai 174 yayin da PDP tana da 153.

To sai dai wasu wakilai biyu daga APC sun koma PDP kana kuma wasu biyun daga PDP suka koma APC. Duk da wannan canje-canjen lissafin bai sake ba. Da aka tambayi Ado Doguwa dan majalisar da tuntuni ya fice daga PDP zuwa APC sai ya ce canza shekar 'yan APC biyu karfin gwiwa ma ya kara masu. Ya ce yanzu ne idanun 'yan Najeriya zasu bude domin da an ce idan ka bar wata jam'iyya ka koma wata kujerarka ta salwanta to yanzu wasu sun shiga PDP yaya ke nan?

Dangane da canje canjen shugabanci da PDP ke yi ya ce ba zai sake komi ba domin PDP ta riga ta shiga rudun da ba zata fito daga ciki ba. A nashi ra'ayin PDP ta mutu. Sabon shugaban PDP ya ce shugaban zaman makoki ne.

Sai dai duk kurar canji dake kadawa a majalisar Ado Doguwa ya ce ba zasu canza kakainsu da mataimakinsa ba domin sun gamsu da yadda suke aiwatar da ayyukansu. Tunanensu na neman a gyara kasar daya yake da nasu a jam'iyyar APC kuma dokokin Najeriya da na zauren majalisa basu hanasu cigaba da zama kan mukamansu ba.

A majalisar dattawa wata majiya ta ce an samu sa hannun sanatoci 16 da suke son su koma APC.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hayaniya ta Tashi a Zaman Farkon Majalisar Wakilan Najeriya - 3:59