Abun da ya faru tamkar fadi ne da Alhaji Bamanga Tukur ya yiwa sabon shugaban jam'iyyar. Da yake jawabi bayan zabensa ya ce ya tuna cewa duk lokacin da ya duka ya gayar da Alhaji Bamanga Tukur sai ya ce masa kada ka yi garaje. Zan mika maka ragamar shugabancin jam'iyyar nan.
Manyan 'yan PDP suna ganin Alhaji Mu'azu zai iya dawo da wadanda suka fice daga jam'iyyar musamman tun da ya karfafa fitar da gwani kafin tsayar da dan takara. Hakan ya nuna matukar shugaba Jonathan zai tsaya takarar shugaban kasa to dole sai ya fuskanci hamayya. Haka ma zata faru da masu takarar gwamnoni da sauran mukamai.
Onarebul Inuwa Dauda kakakin majalisar dokokin jihar Gombe kuma shugaban kakakin dokoki na majalisun Najeriya ya ce zai bada gudummawa wurin tattaro duk 'ya'yan jam'iyyar su zo su hada kai a cigaba da ba jam'iyyar goyon baya domin su cigaba da samun nasara da kuma dorewar tattalin arzikin kasar.
Kafin zaben sabon shugaban shugaba Jonathan ya ce lallai a toya komi gaban 'yan jarida, kada a yi rufa rufa. To yanzu tambaya ita ce wadanda suka fice zasu dawo ne tun da an samu sabon shugaba wanda ya yi alkawarin shimfida adalci? Alhaji Ado Doguwa daya daga cikin wadanda suka canza sheka zuwa APC ya ce canza Bamanga Tukur daya ne daga cikin abubuwa da yawa da suka bukaci a gyara. Sun bada dama a gyara amma yanzu damar da suka bayar ta wuce. Ya ce jam'iyyar PDP da ya sani can baya ta mutu. Ya jawo hankalin Mu'azu ya duba tarihin PDP. Babu shugaban da ya fara lafiya ya kuma kare lafiya tun daga lokacin da aka kafata. Kujerarar da ya dauka yanzu ba abun a yi masa murna ba ne abun a jajanta masa ne.
Ga karin bayani.