Hauka Maganin Ki Allah

An kame wani mutum ‘dan jihar New Mexico dake Amurka, kan laifin satar motar jami’in ‘dan sanda alokacin da yake zagaya gari ba tare kaya jikin sa ba.

Wani ‘dan sandan karamar hukumar Curry ne ya karbi kiran cewa wani mutum na yawo zir akan tituna a ranar hudu ga watan Yuli, inda ya sami mutumin mai shekaru 37 da haihuwa mai suna Jesus Tarango, jami’in ya fadi cewa Jesus na nuna wani irin hali, harma yana cewa an bashi guba ne.

Jami’an sun zaunar da mutumin amma sai ya mike ya fara zagaya motoci.

Hotan bidiyon ‘yan sanda ne ya nuna lokacin da shi Jesus ya shiga ‘daya daga cikin motar ‘yan sandan ya sheka da guda. Wani ‘dan sanda ne ya kama Jesus bayan da ya tsaya a filin ajiye motoci na wani asibiti.

An dai baiwa Jesus kulawa ga raunikan da yaji kafin ya hadu da ‘yan sandan, yanzu haka ana tuhumar sa da wasu laifuka masu yawa, ciki kuwa harda laifin satar abin hawa da tserewa ‘yan sanda, za’a iya sakin sa a belin dala dubu 12.