Bincike ya nunar da cewar, matasa na amfani da shafin sada zumunci na Facebook, wajen ilmantar da kansu da nagartattun, muhimman darussa, batare da sunje makaranta ba. Matasannan kan sakansu cikin wasu mahawarori da wasu kan rubuta a shafinsu na Facebook in, wanda za’aga cewar matasa kan bada tasu fahimtar, wanda take dai-dai ko take fin ta wadansu yara ma da sukaje makaranta.
Mafi akasarin tattaunawar da matasannan kanyi ta sa kai, na maida hankaline a fannin bincike na kimiyya da fasaha. A cewar wannan marubucin Mr. Cheistine Greenhow, Ita tattaunawar sakai da matasa kanyi, na kara fahimta garesu a wasu darussa masu wuyar koyo. Domin kuwa shafin Facebook ba kawai don zumunci aka kirkireshiba, harma da ilmantar da juna wasu abubu na dan-daban daga wata nahiyar zuwa wata.
A wani rahoto da aka buga a wata jaridar binciken hallayan dan’adam a fannin ilimin kwamfuta. An gwada wasu dalibai masu shekaru 16 zuwa 25 wadannda suka sa kansu a wani gwaji da aka gudanar, wanda aka yi wata muhawara da tashafi darasin chanjin yanayi, binciken dai yabayyanar da cewar yaran sun nuna jin dadinsu da shiga cikin wannan binciken, kuma sun bayyanar da basirarsu kamar yadda, wasu yara wadanda sukaje aji aka koyar dasu. Ashe kuwa ba sai matasa kawai sunje aji an koyar dasu ke nufin sunsan abuba, wanna na nuni dacewar kowane yaro nada irin baiwar da Allah yayi masa.
Shidai dai marubucin, yace akwai bukatar samamar da irin wadannan guraben nishadantarwa ga yara, kuma da basu damar su bayyanar da irin tasu hazakar da fadin ra’ayoyinsu. Domin ta hakama zasu samu haduwa da wasu wadannda sukafisu basira, daga nan sai a yi kokarin ilmantar da juna, wanda ta haka za’asamu nagartaciyar al’uma.