Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Najeriya ta karu zuwa kaso 33.88 cikin 100 a watan Oktoban da ya gabata, daga kaso 32.7 cikin 100 da aka gani a watan Satumbar da ya gabace shi, inda ya nuna samun karin kaso 1.18 cikin 100 a bisa kididdigar wata-wata.
Hakan na kunshe ne a rahoton sauyin farashin kayan masarufi bayan wani lokaci da hukumar kididdigar Najeriya (NBS) ta fitar a yau Juma’a.
Hukumar ta alakanta tashin farashin da karuwar kudin sufuri da farashin kayan abinci.
A bisa kididdigar shekara zuwa shekara kuma, hauhawar farashin kayan masarufin ta karu da kaso 6.55 cikin 100 a kan kaso (27.33%) da akan gani a watan Oktoban 2023.
Hakan na nufin hauhawar farashin ta karu a watan Oktoban shekarar da muke ciki idan aka kwatanta da yadda yake a shekarar da ta gabata.
A bisa kididdigar wata zuwa wata kuwa, NBS ta kara da cewa hauhawar farashin ta kai kaso 2.64% a watan Oktoban 2024, wacce ta dara mizanin da take a watan Satumbar da ya gabace ta (2.52%) da kaso 0.12 cikin 100.
Hakan na nufin cewa a watan Oktoban 2024, matsakaiciyar hauhawar farashin kayan masarufi ta dara yadda take a watan Satumbar da ya gabace shi.