Hukumar ta ce hauhawar farashin kayaki a Najeriya ya karu, inda ya kai kaso 34.19% cikin 100% a watan Yuni, kuma hakan na nuni da cewa, ba a taba fuskantar irin wannan hauhawar farashi kayaki a shekarar nan ba, wanda kayakin masarufi na gaba-gaba wajen ingiza hauhawar farashin, a cewar rahoton.
Hukumar ta NBS, ta ce hauhawar farashin kayakin Masarufi, da suka hada da Gero, Masara, Man-Gyada, Man-Ja, Doya, Dankali, Kifi da dai sauransu, na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen hauhawar farashi kayaki a kasar, inda farashinsu ya kai kaso 40.87% bisa ma’auni.
Rahoton na NBS, ya kara da cewa farashin kayakin Masarufin ya karu da kaso 11.31% bisa ma’auni, cikin shekara daya, idan aka kwatanta da yadda farashinsu yake a watan Yunin shekarar da ta gabata.
A farkon makon nan ne, aka ji Ministan Sadarwa Mohammed Idriss yake bayyana cewa, gwamnatin Tarayya ta ba gwamnonin kasar, buhunan shinkafa su rabawa mabukata a Jihohinsu, domin rage musu zafin raɗaɗin da suke ciki.
Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna