Harry Kane Ke Kan Gaba Wajan Jefa Kwallaye

A cigaba da fafatawa da ake yi a gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya a kasar Rasha, matakin wasan rukunin zagaye na biyu a jiya Kasar Ingila ta lallasa Panama da kwallaye 6-1, Japan sun tashi canjaras 2-2 da kasar Senegal, Poland ta sha kashi a hannun Colombia daci 3-0.

A yau kuma ana cigaba a matakin zagaye na uku a wasannin rukuni wanda shine na karshe a wannan matakin rukunin

Dan wasan kasar Ingila Harry Kane shi yake kan gaba wajan jefa kwallo a raga inda ya zurara kwallaye 5, a wasa biyu sai Cristiano Ronaldo, na Portugal, da Romelu Lukaku daga Belgium, masu kwallaye 4, Denis daga Rasha da Diego Costa Spain kwallaye 3.

Ahmed Musa, a Nigeria, Luka Modric Croatia, Eden Hazard Belgium dukkan su kwallaye 2, inda aka bada Katin gargadi (Yellow cards) 99 Jan kati (Red cards) 2 ‘yan wasan da suka samu Jan Katin sune Jerome Boateng, na Germany a wasansu da Sweden sai Sanchez daga Columbia, wasansu da Japan.

Your browser doesn’t support HTML5

Harry Kane Na Kan Gaba Wajan Jefa Kwallaye