Harris Ta Yi Gangami A Washington, Trump Ya Yi Nasa A Pennsylvania

Kamala, (Hagu) Donald Trump (Dama0

Dukkan ‘yan takarar biyu, na nuna rashin amincewa da junansu inda suke nuna daya bai cancanci ya jagoranci kasar na wa’adin mulki na shekaru hudu ba.

Yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka wanda alkaluma suka nuna ana tafiya kankankan, ‘yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democrat Kamala Harris da Tsohon shugaban kasa Donald Trump na jam'iyyar Republican sun ci gaba da caccakar juna a gangamin yakin neman zabensu.

Kamala Harris, ta gabatar da abin da ta kira "jawabin rufe muhawararta" ga masu kada kuri’a da maraicen ranar Talata a kusa da Fadar White House da ke nan birnin Washington D.C.

“Mun san wane ne Donald Trump, shi ne mutumin da ya tsaya a daidai wannan wurin kusan shekaru hudu da suka gabata, ya tura gungun mutane dauke da makamai zuwa ginin majalisar dokoki don su sauya sakamakon zaben da aka yi mai sahihanci.” In ji Harris.

Shi kuwa Trump ya gudanar da yakin neman zabensa ne a jihar Pennsylvania, daya daga cikin jihohi bakwai da ake fafatawa wajen neman kuri’u, wadanda mai yiwuwa su za su nuna akalar sakamakon zaben kasar baki daya.

“Idan aka zabe ta ta shiga ofis, kasarmu ta kade, na tabbata cewa kasarmu ta kade. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa kasuwar hannayen jari take faduwa.” Trump ya ce.

Dukkan ‘yan takarar biyu, suna nuna rashin amincewa da juna a matsayin wanda bai cancanci ya jagoranci kasar na wa’adin mulki na shekaru hudu ba.

Kazalika suna neman duk wata ‘yar dama don zaburar da masu kada kuri’a wadanda ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba, a abin da ka iya zama zaben da aka fi tafiya kankankan tsakanin ‘yan takara cikin gomman shekaru.

Kuri’un jin ra’yoyoin jama’a da aka gudanar sun nuna cewa za’a fafata sosai a zaben, yayin da Harris da Trump ke kunne doki a wasu jihohi masu muhimmanci ko kuma da dan tazara kadan a gaba ko baya.