Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris, Trump Sun Kara Dukufa Wajen Neman Kuri’u Yayin Da Aka Tunkari Ranar Zabe


Donald Trump (Hagu), Kamala Harris (Dama)
Donald Trump (Hagu), Kamala Harris (Dama)

Yayin da ya rage kasa da makonni biyu a gudanar da zaben shugaban kasa na 2024, Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris sun kai ziyara wasu daga cikin muhimman jihohin da ake kare jini biri jini a lokacin zabe.

Trump wanda ke takara karkashin jam’iyyar Republican ya yada zango a wurare uku a ranar Litinin a jihar North Carolina ciki har da inda ya kai ziyara yankin Ashville da guguwa ta yi ta’adi.

Harris a nata bangaren ta maida hankali ne wajen kai ziyara yankunan da ke wajen gari a jihohin da ke tsakiyar yammcin Afirka da ake gwagwagwa a lokacin zabe inda ta hadu da Liz Cheney ta jam’iyyar Republican.

Trump dai ya ci gaba da caccakar Harris a gangamin yakin neman zaben da ya yi a Greenville da ke jihar North Carolina inda ya kwatanta ta a matsayin “mara hankali” sannan ya ce ba ta da tausayi da kwarin zuciya.

Ya kuma soke ta da neman tallafin kudi a San Francisco da ta yi fama da matsalar ibtila’in guguwa.

“Kamala Harris ba ta da tausayi ko basira ko karfin zuciyar da za ta zama Shugabar Amurka. Sam ba za ta iya aikin ba.” In ji Trump.

A nata bangaren Harris ta ce ya kamata a rika daukar kalaman Trump da muhimmanci maimakon a rika kore su ana musu kallon “abin dariya na wanda ba shi da lafiya.”

“Wasu na kallon kalaman nasa a matsayin abin dariya, abin da yake fada shirme ne. Amma ya kamata a fahimci cewa abu ne da ya kamata a sa masa ido sosai.” Harris ta ce.

Harris ta yi nuni da kalaman Janar Mark A. Milley mai ritaya wanda ya rike mukamin shugaban hafsan hafsoshin sojin Amurka a mulkin Trump na farko wanda ya kwatanta Trump a matsayin “tsattsauran mai mulkin kama karya.”

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG