Mazauna garin Damaturu sun yaba da yadda al'amuran tsaro suka fara yin kyau da kuma yadda jami'an tsaron suke mutunta fararen hula
Al’amuran yau da kullum sun fara komowa kamar yadda aka saba gani sannu kan hankali a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Jihar ta Yobe, tana daya daga cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci a watan Mayu, aka kuma tsinke dukkan layukan wayoyin salula a wani yunkurin murkushe mayaka na kungiyar Boko Haram a yankin.
Wakiliyar Sashen Hausa, Sa'adatu Mohammed Fawu, ta zaga kasuwanni da unguwannin garin na Damaturu, inda ta bayyana cewa jama'a sun fara fitowa sosai tare da nuna alamun sake jiki, ba kamar watannin baya ba.
Wani mazaunin garin na Damaturu, yace wannan shi ne karo na farko cikin watanni 6 da yake iya shiga cikin wasu unguwannin da a can baya kusan kowa yake tsoron shiga don gudun hasarar rai. Ya yaba da matakan tsaron da aka dauka, da kuma yadda jami'an tsaro suke mutunta jama'a.
Wata mace ma da ta ttauna da wakiliyar ta mu ta yaba ma jami'an tsaron bisa yadda suke hulda da jama'a irin ta mutuntawa.
kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa, Leftana Eli Lazarus, yace sun shimfida tsare-tsare da yawa na gudanar da ayyukansu wadanda suka hada har da na hulda da jama'a fararen hula. Ya roki jama'a da su ci gaba da taimaka musu domin a samu a kammala wannan aiki kowa ya koma rayuwarsa ta yau da kullum.

Your browser doesn’t support HTML5