A cikin wani sakon email da ya aikawa sashen Hausa na Muryar Amurka, Muhammad Marwana yace su nan daram kan bakarsu ta tattaunawa da kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa domin samo madafa ta yin sulhu a Najeriya.
A yayin da yake misali da irin cin zarafi da kuma kisan da yace jami'an tsaron Najeriya sun yi ma iyalinsa shi kansa, Marwana yace wannan kwamiti na gwamnatin Najeriya ya kunshi "zababbun adalai wadanda su na sane da cin zarafin da aka yi mana a baya. Hakika abinda aka yi mana...shi ya sa mu ma muka maida martani maras dadi."
Marwana ya ci gaba da cewa ganin irin yanayin da al'ummar Musulmin Najeriya suka tsinci kansu a ciki, ya tattara kwamandojin kungiyar domin a yafe ma juna, kuma a fuskanci juna, domin "ya zamanto babu gaba a ttsakaninmu da mutane" in ji shi.
Marwana ya shawarci jama'a da su bar jin maganganun Shekau, har ma yace idan har zai iya, ya cika barazanar da yayi ta kai hare. Yace duk mutumin da Shekau yayi masa barazana, to yaje yayi barcinsa har da "munshari, domin babu abinda zai faru a kansa da iznin Ubangiji."
Yace jama'a su zuba idanu su ga abinda zai faru a tsakaninsu da Shekau.
Marwana yayi wasu zarge-zarge game da Abubakar Shekau a cikin wasikarsa.