Da a Najeriya ana daukan yara daga Legas zuwa Maiduguri ko Sokoto ko kuma daga Gusau zuwa Oyo ko daga Kano zuwa Ibadan ko dai wani gari daban. To yanzu a halin da ake ciki iyaye na shakkan barin 'ya'yansu su yi nisa da su ba domin komi ba domin rashin tsaro har ma a makarantu.
Taron shugabannin ilimin ya tabo batun samarda malamai nagatartu a makarantun framare da sakandare ba na bogi ba. Kamata yayi kafin a dauki malamai a bincikesu. A tabatar suna da takardun shaida na ilimin da suke ikirarin sun samu kana a bi digdigi. Sun yi misali da jihar Pilato inda malamai fiye da dubu daya suka ce sun yi karatu a makarantar horar da malamai a Gindiri. Da aka bincika mutane takwas ne kawai suka yi karatu a makarantar. Duk sauran na bogi ne. Domin haka dole a binciki malamai kafin a daukesu aikin koyas da yara.
Mustafa Nasiru Batsari nada karin bayani.