kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya, Birgediya-janar Chris Olukolade, ya fadawa VOA cewa an maido da layukan salula jiya jumma'a a Jihar Borno, a bayan da aka sake maida su a jihohin Adamawa da Yobe.
Yace jami'ai sun yi imani da cewa an samu cimma nasarori a wadannan jihohi uku ta yadda mutane zasu iya komawa ga gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Amma kuma wani dan jarida mai suna Abdeulkareem Haruna, ya fadawa VOA cewa an maido da layukan wayoyin na salula na tsawon awa biyu tak, sai kuma suka sake daukewa a jihar ta Borno.
Shugaba Goodluck Jonathan ya tura karin sojoji zuwa jihohin uku a tsakiyar watan Mayu, a bayan da aka samu karin hare-hare daga kungiyar Boko Haram, wadda aka dora ma alhakin mutuwar dubban mutane a cikin shekaru hudun da suka shige.
An rufe dukkan layukan wayoyin salula a jihohin uku, domin gurgunta hanyoyin sadarwa a tsakanin mayakan Boko Haram.
Rufe layukan ya sa ana fuskantar wahala sosai wajen tabbatar da gaskiyar ikirarin da sojoji keyi cewa sun wargaza sansanonin 'yan Boko Haram, sun kuma kashe ko sun kama mayakan kungiyar da dama.