Harkokin 419 Na Janyo Asarar Biliyoyin Daloli

Tsakanin Najeriya da sauran kasashen duniya ana asarar biliyoyin dalar Amurka, sakamakon ayyukan ‘yan damfara da aka fi sani da ‘yan 419, ko Yahoo-yahoo Boys.

Wani bincike da Majalisar Dokoki ta Najeriya ta yi ya nuna cewa kasar na asarar fiye da Naira biliyan 127 a duk shekara, bisa laifukan da suka shafi zamba ta kafofin sadarwar zamani.

Bincike dai ya nuna cewa bayan kasar Amurka da Birtaniya, Najeriya itace kasa ta uku a ayyukan zamba ta kafofin sadarwa da ake kira Internet Crime da turanci.

Domin yaki da zamba Najeriya ta kafa hukumar EFCC shekaru fiye da goma da suka gabata, to sai dai kuma hankalin hukumar ya karkata wajen yaki da masu cin hanci da rashawa na siyasa. Masu aikata zamba ta yanar gizo sun mayar da hankalinsu ne kan manyan kamfanoni na cikin gida da na ketare.

Wani rahoto da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, sashen masu yaki da zamba ta yanar gizo ya nuna cewa irin wadannan kamfanoni na cikin Najeriya da waje daga shekara ta 2013 zuwa 2016 sunyi asarar dalar Amurka biliyan 5.3

Yanzu dai da hukumar EFCC ta fi mayar da hankali kan ‘yan siyasa masu masu zagon ‘kasa ga tattalin arzikin Najeriya, masana da sauran kasashe na ganin akwai bukatar hukumar ta kara mayar da hankali kan ‘yan 419 kamar yadda aka sansu a Najeriya.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Asarar Biliyoyin Dalar Amurka Sakamakon ‘Yan 419 - 3'51"