Talata nan shugaba Mohammad Buhari na Najeriya ya kaddamar da taron kungiyar gwamnonin jihohin dake yankin tapkin Chadi.
Gwamnonin sun hada da na kasashen Nijar, Kamaru, Chadi na Najeriya. Taron gwamnonin jihohin dake kewayen yankin tafkin Chadi shi ne irinsa na farko. Manufar kafa kungiyar ita ce ba gwamnonin daman tattaunawa da junansu akan abubuwan da suka shafesu, musamman domin sake farfado da tafkin da ma yankin gaba daya.
Gwamnan Borno Kashim Shettima shi ya wakilci shugaban Najeriya, Muhammad Buhari wanda ya kaddamar da taron kungiyar na kwana biyu.
A jawabin na shugaban kasa, ya ce akwai mutane fiye da miliyan 55 da suka dogara ga tafkin wajen samun abincinsu da tafiyar da rayuwarsu. Tafkin shi ne mafi girma a nahiyar Afirka da yake da iyaka da kasar Kamaru da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.
Mutanen dake yankin sun dogara ne da noma da kamnun kifi da kiwo wajen bunkasa tattalin arziki. Zamu yi iyakacin kokarinmu mu sake farfado da yankin domin jama'a su ci gaba da rayuwarsu cikin walwala da kwanciyar hankali, a cewar Shugaba Muhammad Buhari ta bakin gwamnan jihar Bornu
Dr Ibn Chambers wakilin Majalisar Dinkin Duniya, wanda yake kula da kasashen Afirka ya ce kodayake ba za'a ce an gama da kungiyar Boko Haram ba amma an karya lagwansu kuma kamata yayi a ci gaba da fafatawa dasu. Ya ce suna da kwarin gwuiwa bisa abun da suka ji daga kwamandan sojojin dake yankin saboda, ya tabbatar masu da cewar Majalisar Dinkin Duniya zata ci gaba da bada goyon bayan ta a yakin.
Gwamnan jihar Diffa daga Jamhuriyar Nijar Alhaji Muhammadou Bakabe ya ce manufarsu ita ce su hada karfi da karfe su yaki ta'addanci domin jihohin dake yankin su samu lafiya.
Dangane da ko an samu dawamammen zaman lafiya a yankin Manjo Janar Lucky Irabor kwamandan sojojin kasashen yankin tafkin Chadin ya ce babu inda za'a ce an samu zaman lafiya gaba daya, amma ana samun shi sannu a hankali.
Ambassador Ahmed Shehu shugaban kungiyoyi dake zaman kansu a yankin tafkin Chadin wanda kuma ya gabatar da kasida a wajen taron, ya yi magane akan yadda ake rabawa mutane abubuwan da basu bukata. Ya ce idan za'a taimakawa mutane a basu abun da suke bukata
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum