Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Khalifa Isyaku Rabiu Ya Rasu Yana Da Shekaru 93


Khalifa Isyaku Rabi'u
Khalifa Isyaku Rabi'u

Malamin addinin musulunci kuma hamshakin attajiri Khalifa Isyaku Rabiu ya rasu a wani asibiti dake London kasar Birtaniya yana da shekaru 93 da haihuwa kuma ana sa ran za’a yi jana’izarsa gobe Alhamis a Kano

Malami kuma attajiri Khalifa Isyaku Rabiu ya rasu ne a wani asibiti a Birnin London a kasar Birtaniya.

Jama’a sun soma yin tururuwa zuwa gidan marigayin dake Goron Dutse a cikin brinin Kano domin yiwa juna ta’aziya.

Wazirin Kano murabus Shaikh Nasiru Muhammad Nasir na cikin sahiban Khalifa Isyaka Rabiu. Ya ce sun rayu tare sun kuma taso tare kuma a wurin malami daya suka yi karatu kafin Allah ya karbi ransa bayan sallar magariba jiya. Ya bayyana shi Khalifa Isyaku a matsayin wanda ya haddace Kur’ani yana karantashi a gida, akan hanya da ma ofishinsa kana kuma gashi attajiri, mai son mutane da yawan yin kyauta.

Shi kuawa alaramma Malam Dauda Loko Makera a cewarsa rashi ne ga dukannin mahaddacin Kur’ani da dukannin wadanda suke yiwa Kur’ani hidima da duka masu son su koyi Kur’ani. Ya ce rashi ne a garesu ga baki daya.

A cikin wata sanarwa da kwamishanan labaran jihar Kano Muhammad Garba y araba a daren jiya gwamnatin jihar ta bayyana rasuwa attajirin kuma shaikh a matsayin asara ga muslman duniya gaba daya.

Ana sa ran za’a yi jana’izarsa gobe Alhamis bayan an kawo gawarsa daga Birtaniya.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG