Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Burutai shi ne ya yi wannan gargadi yayin zirar gani da ido da ya kai zuwa Mubi don duba asarar da aka yi sakamakon harin kunar bakin wanken da aka kai wani Massalaci ,cikin kwanakin nan.
Rayuka da dama ne dai suka salwanta a makon jiya,biyo bayan tashin wasu tagwayen bama-bamai a garin na Mubi dake zama cibiyar kasuwancin jihar Adamawa,kuma gari na biyu mafi girma a jihar.
A ma dai ziyarar gani da idon da ya kawo, babban hafsan sojin, Janar Tukur Yusuf Burutai ya ce za’a kara yawan sojoji a yankin domin dakile hare haren da yan bindiga masu tada kayar baya na Boko Haram,da a baya suka kafa daularsu ta Madinatul Islam a garin.
Burutai,wanda ya soma da fadar sarkin Mubi,Abubakar Isa Ahmadu,ya bukaci jama’a da su zama masu sa ido,da kuma kai rahoton duk wani da basu amince da take takensa ba ga hukumomin tsaro.
‘’Dole fa,muke sa ido domin gano yan kunar bakin wake dake shiga cikin al’umma don tu’annati.Wannan aiki ba wai kawai na jami’an tsaro ba ne,a’a,kowa na da rawar da zai taka.
‘’ Sukan yi shigar burtu,don sauya kama.Wani lokaci sukan yi shiga na mahaukata,sukan sa kaya da yawa a jikinsu,shiga dai na mara gaskiya,don haka a kula’’a cewar Janar Buratai
Da yake mai da jawabi,mai martaba sarkin Mubi,Alhaji Abubakar Isa Ahmadu,ya ce yanzu haka masarautar da kuma shugabanni a yanki sun kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a,na daukan matakan tsaro domin hana sake aukuwan abun da ya faru.
‘’ Yanzu haka,mun dau darasi,don haka muka kaddamar da fadakarwan,kuma zamu ci gaba da hada kai da sauran jami’an tsaro,muna fatan za’a cigaba da bada hadin kai.’’
Wannan dai na zuwa ne yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci wadanda suka samu raunuka da yanzu ke kwance a asibiti inda har ya bada gudummawar naira miliyan goma ga gidauniyar tallafawa marasa galihu na asibitin tarayya dake Yola,FMC-Yola,don jinyan wadanda suka samu raunuka.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum