Al'ummar kauyen Tatara na karamar hukumar karu ta jihar nassarawa sun fada cikin firgici sakamakon harin 'yan bindigar da ya hallaka mutane 7.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Sp Ragman Nansel, ne ya bayyanawa tashar talabijin ta channels cewar harin ya afku a daren Asabar din da ta gabata.
Ya kara da cewar 'yan sanda sun samu kiran gaggawa kuma nan take, kwamishinan 'yan sandan jihar, Shettima Muhammad, ya jagoranci tawagar jami'ansa zuwa wurin inda suka gano gawawwaki 7 tare da bin sawun maharan abinda ya tilasta musu yin watsi da baburansu 9.
Ya ci gaba da cewa nan take kwamishinan 'yan sandan ya kira taron masu ruwa da tsaki inda ya yiwa iyalan wadanda suka mutu ta'aziya tare da bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.
An tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin domin tabbatar da tsaro sannan an tsara cewar gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule zai ziyarci wurin.