Rundunar 'Yansanda ta jahar Barno tatabbatar da mutuwar mutane akalla 18 a garin Kwanduga, sakamakon wani harin kunar-bakin-wake da suka kai a wata kasuwar kifi dake garin.
Wannana lamarin ya auku ne da misalin karfe 8:30 na dare ranar jumma'a, lokacin maharan su biyu ko uku, maza da mata suka shiga kasuwar suka tayar nakiyoyi da suke jikin su.
Kakakin rundunar 'Yansandan jahar ASP Joseph Kwaji, ya tabbatarwa wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu, yana mai cewa mutane 18 da 'yan kunar bakin wake biyu harin ya halaka. Ya kara da cewa wasu mutane 22 sun jikkata sakamakon harin. Tuni an kai su asibitoci daban daban dake yankin don jinya.
Wannan shine karon farko da aka kaiwa harin harin a bana, wadda yasha fuskantar munanan hare hare a baya.
Wani mazaunain garin na kwanduga a nasa bayanin yaa gayawa Haruna Dauda cewa, cikin wadanda harin ya rutsa dashi har da wani soja, wnda watakil yace kasuwar don shan shayi.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5