Harin Da Aka Kai Da Jirgi Mara Matuki A Libya Takalar Yaki Ne-Siala

Mohamed Taher Siala

Ministan Harkokin Wajen Libya ya fada jiya Litinin cewa harin da aka kai da jirgi mara matuki da ya yi sanadin mutuwar mutane akan kamfanin biskit a Tripoli babban birnin kasar, na iya zama laifin yaki.

Mohamed Taher Siala ya fadawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da suke taron da suka saba gudanarwa don tattauna halin da kasashen Arewacin Nahiyar Afrika suke ciki cewa, “Wannan laifin yaki ne da aka kitsa shi,”.

Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Ghassan Salame, ya fadawa kwamitin sulhun ta hanyar tattauna a bidiyo daga makwabciyar kasar Tunisia cewa, akalla mutum goma suka mutu da kuma sama da mutum 35 suka ji raunuka a harin na ranar Litinin.

“Abinda ya bayyana dayawa daga cikin wadanda suka mutu bakin haure ne, amma kuma akalla mutum biyu ‘yan Libya ne, A cewar Salame. “Ko da kuwa harin an kaishi ana sane ne da ya auna kamfanin ko an kaishi ba tare da nuna banbanci ba, ya zama an aikata laifin yaki,” ya kuma kara da cewa ya kamata a tuhumi ministan harkokin wajan kasar.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaiwa.