Bisa dukan alamu, Ministocin Kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da suka bukaci bude iyakokin Najeriya da aka rufe tun watan Agustan bana cikin gaggawa, sun fice cikin fushi daga taron da Wakilan Gwamnatocin Kasashen da ke Makwabtaka da Najeriya suka yi a Abuja akan halin da kasashen suka tsinci kansu tun bayan rufe iyakokin Najeriya,domin kuwa Ministan Kula da harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama ya karanata wa Manema Labarai Jawabin bayan taron daga shi sai 'yan'uwansa na cikin gida.
Kasar Nijar da ke Makwabtaka da Najeriya ta bangaren Arewa ta bayana cewa rufe iyakokin na kasa, ya jawo mata asarar makudan kudade da yawan su ya kai CEFA miliyan 40, kimanin dalar Amurka miliyan 67, Kwatankwacin fiye da Naira miliyan 24 a Kudin Najeriya.
Ministan Kula da Harkokin Cikin gida na Nijar Mohammed Bazoum da ya fice kafin a gama taron ya ce Najeriya ta dauki mataki mai zafi na rufe kan iyakokin ta da Kasashen uku ne a bisa abinda ta kira matsalolin da ta ke fuskanta na fasa kwabri, su ma kansu Nijar wanan matsala tana shafan su, shi ya sa a yau suka taru domin lalubo mafita wacce ba za ta cutar da kowace kasa ba.Saboda matsalar fasa kwari ta addabi kasashen da ke makwabtaka da Najeriyan ne duka.
To saidai Karamin Ministan Hulda da Kasashen waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada ya bayyana wa manema labarai cewa wuni muhimmin mataki da taron ya dauka shi ne na nada wani komiti na musamman da ke dauke da jami'an Kwastan, da na jami'an Shige da Fice,da na Hukumomin tsaron kasashen uku, da zai yi rangadi da sintiri a kan iyakokin kasashen sannan ya bada rahoto da Najeriya za ta duba yiwuwar bude iyakokin ta.
Amma ga mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum Aminu Jumare yana ganin ba a bi dokokin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wajen rufe iyakokin Najeriya ba.
Nan da makonni biyu na gaba Komitin Kula da harkokin tsaro za ta sake wani taro a Abuja babban Birnin Najeriya.
Ga karin bayani daga Madina Dauda
Facebook Forum