A jamhuriyar Nijar masana doka da ‘yan siyasa na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da komawar tsohon Firai Minista Hama Amadou gida, bayan shafe shekaru da dama yana gudun hijira a kasashen waje, sakamakon zarginsa da hannu a wata badakalar jarirai.
Kwana daya bayan dawowar Hama Amadou gida bayanai na nuna cewa mahimman batutuwa biyu ne suka ba shi kwarin gwiwar katse gudun hijirar da yake yi a ketare, wato zaman makokin rasuwar mahaifiyarsa, da batun hukuncin da wata kotun Yamai ta yanke masa a watan Okoban 2017.
Zaman sulhun da ake shirin farawa a nan gaba a tsakanin ‘Yan Adawa da masu mulki, na daga cikin dalilan da ake ganin sun taimaka wajen dawowar Hama Amadou gida.
Jagoran ‘yan adawa Hama Amadou mutun ne da ake yi wa kallon ya na da gogewa a siyasa saboda haka wasu ke ganin dawowarsa gida abu ne da zai iya dagula wa jam’iyyar PNDS Tarayya lissafi.
Ga rahoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum