Wani Harin Bindiga A Cocin Jehovah Witness A Jamus Ya Yi Sanadin Asarar Rayuka

Deadly shooting in Hamburg

An yi harbe-harbe a cikin wani gini da ‘yan cocin Jehovah’s Witness suke amfani da shi a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus a yammacin jiya Alhamis, kuma mutane da yawa sun mutu wasu kuma sun jikkata, a cewari ‘yan sanda.

An yi harbe-harben ne a gundumar Gross Borstel, mai nisan ‘yan kilomitoci daga tsakiyar birnin na biyu mafi girma a Jamus.

"Mun dai san cewa mutane da yawa sun mutu a nan; wasu da yawa kuma sun jikkata, an kai su asibitoci," a cewar Holger Vehren kakakin rundunar 'yan sandan yankin. Sai dai ya ce ba shi da wani bayani kan munin raunin da mutanen suka ji.

Ya ce ba shi da wani bayani kan munin raunin da wadanda suka jikkata suka samu.

Deadly shooting in Hamburg

'Yan sanda ba su tabbatar da rahotannin kafofin yada labaran Jamus ba, wadanda ba a bayyana majiyarsu ba, na mutane shida ko bakwai da suka mutu.

Wurin da aka yi harbin shi ne wurin ibadar mabiya darikar Jehovah Witness, gini na zamani mai hawa uku da ke kusa da wani shagon gyaran motoci.

Magajin garin birnin Hamburg Peter Tschentscher ya wallafa a shafinsa na twitter cewa labarin ya tayar da hankali kana ya jajantawa 'yan uwan wadanda abin ya shafa.

Jehovah Witness da na cikin coci na duniya, da aka kafa a Amurka a karni na 19 kuma mai hedkwata a Warwick, New York. Tana da'awar kasancewa a duk fadin duniya da mabiya kusan miliyan 8.7, tare da kusan 170,000 a Jamus.