Sakatariyar Sojin Amurka, Christine Wormuth, ta shaidawa mahalarta wani taro a Cibiyar Kasuwancin Amurka (AEI) cewa, "Ni da kaina ba ni da ra'ayin cewa wani mummunan hari kan tsibirin Taiwan na gab da zuwa. Amma a zahiri dole ne mu shirya, don mu kasance cikin shiri don yin yaki da cin nasarar wannan yakin."
Abubuwan da ke cikin shirin sun hada da sanya karin dakaru a yankin Asiya da kuma ba su kayan aikin da aka inganta, wadanda suka hada da jiragen ruwa zuwa gabar teku da manyan makamai masu karfin gaske, wadanda yawancinsu za a riga aka kafa su a yankin.
Ta ci gaba da cewa "Manufarmu ita ce mu guje wa duk wani yaki kan diyauci a yankin Asiya," in ji Wormuth. "Ina ganin hanya mafi kyau don guje wa yakin, ita ce a nuna wa kasar China da kasashen yankin cewa za mu iya lashe wannan yakin."
Wormuth ta zayyana muhimman abubuwa guda uku na abin da ta kira shirin da sojojin Amurka suka yi don dakile irin wannan yaki, inda ta fara da batun hadin gwiwa tare da kawayen kasashen waje da abokan hulda don "rikitar da" shawarar shugabannin kasar China suka yanke.
Na biyu, in ji ta, Sojojin suna shirin gina "cibiyoyin rarraba kayan aiki" a yankin don tara kayayyaki da mai, mai yiwuwa a fara da kasar Australia." Wormuth ta kuma ba da sunan Japan a matsayin wurin wurin da za a iya yin hakan, kuma ta ba da shawarar cewa za a iya adana kayan aikin da ba na yaki ba a Philippines da Singapore.
Abu na uku na shirin, shi ne sanya rundunonin da za a iya gani, masu karfin fada a ji a yankin, in ji Wormuth. "Manufarmu ita ce a sami dakarun soji a cikin yankin Indo-Pacific watanni bakwai zuwa takwas a cikin shekara."