‘Yar kasuwa Ogechi Egemonu da ke zaune a Legas tana sayar da agogo, takalma da jakankuna na sama da naira 500,000 ($ 1,219) ta shafin Twitter a kowane mako.
Yanzu, da gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin, Egemonu ba ta rasa yadda za ta bullowa lamarin.
“Kafar sada zumunta ita ce wurin da nake cin abinci." "Na dogara ne da kafafen sada zumunta ne wajen neman abin da zan rufawa kaina asiri." Egemomu ta fadawa Reuters.
Wuraren kasuwanci manya da kanana a Najeriya, wacce ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka da tattalin arziki mafi karfi, na ci gaba da fuskantar kalubale sanadiyyar dakatar da kafar sada zumuntar.
Najeriya ta sanar da dakatarwar ne a ranar 4 ga Yuni, kwanaki bayan da dandalin ya cire wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa, wanda ya yi barazanar hukunta masu ballewar yankin. Galibin kamfanonin sadarwa sun rufe hanyoyin bude shafin.
Hukumomin kasar sun ce sun rufe kafar sada zumuntar ce, saboda tana barazana ga zaman lafiyar Najeriyar, la'akkari da irin sakonnin da take bari ana wallafawa.