Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Aiwatar Da Sauye-sauye Don Saukaka Kasuwanci


Alhaji Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed

Gwamnatin Najeriya na aiwatar da sauye-sauyen da za ta karfafa nuna gaskiya da saukake gudanar da kasuwanci a kasar da ke Yammacin Afirka.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya ce gwamnatin ta kuma karfafa kokarin yaki da cin hanci da rashawa don tsabtace dukkan bangarorin tattalin arzikin kasar inda ake yin zargin cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa, sannu-a-hankali, nan gaba 'yan Najeriya za su ga kyakkyawan sakamako na matakan da ake aiwatarwa don yaki da rashawa.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan da masu suka su ka zargi gwamnati da cewa ba ta yin wani abin a zo a gani ba wajen dakile cin hanci da rashawa.

Sun kuma ambaci ƙananan ƙididdigar kwanan nan da ke ƙunshe a cikin sabon rahoton da kungiyar Transparency International ta gabatar kan ra'ayoyin masu saka jari game da cin hanci da rashawa a Najeriya. Amma Mohammed ya ce rahotannin ba gaskiya bane na halin da ake ciki a kasa.

Ya kara da cewa bayanan da kungiyar TI din ta yi amfani da su don bincikensu bai dace ba da halin da ake ciki ba.

Kakakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Kola Ologbondiyan, ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa gwamnati kamar ba za ta iya yakar cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG