Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Tashin Farashin Siminta Ke Janyo Cikas Ga Masu Harkar Gine-gine a Najeriya


Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya
Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya

Kamfanin Dangote na da kashi 60.6 wanda mallakar Aliko Dangote ne, mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka. Sai Lafarge da ke da kashi 21.8 yayin da BUA ke da kashi 17.6

Najeriya na fuskantar matsalar hauhawan farashin siminti, lamarin da masu lura da al’amura suke ce yana haifar da tarnaki ga fannin masu gine-gine a kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

A watan da ya gabata, ‘yan majalisar dokokin kasar suka ce, mamaye harkar sayar da siminti da wasu kamfanoni uku suka yi, na ci gaba da haddasa tashin farashin mahadin na gine-gine.

Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya
Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya

A cewarsu, hakan yana haifar da tarnaki a kokarin da ake yi na farfado da tattalin arzikin kasar wacce ta fi arziki a nahiyar Afirka.

Kashi uku na adadnin mutanen da suka isa yin aiki a Najeriya ba su da abin yi, kuma kasar ta farfado daga komadar tattalin arzikinta ne na biyu cikin shekara hudu a bara.

Kamfanin Dangote na da kashi 60.6 wanda mallakar Aliko Dangote ne, mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka.

Sai Lafarge da ke da kashi 21.8 yayin da BUA ke da kashi 17.6

Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya
Tashin Farashin siminta na janyo cikas ga masu gine-gine a Najeriya

Mamaye harkar sayar da siminti da kamfanonin suka yi, na tattare ne da haramcin shigar da simintin da aka saka a kasar tun shekara 20 da suka gabata, a wani mataki na sa Najeriya zama mai dogaro da kanta a fannin hada siminti.

Kamfanonin simintina sun kara farashinsu a lokacin da Najeriya ta fuskanci komadar tattalin arziki a shekarar 2016 a wani mataki da suka dauka na rufe gibin rashin ciniki da ba sa yi, kuma tun daga lokacin, farashin ya ci gaba da hauhawa. Baya ga haka, akwai korafi da suke yi na tsadar ayyukan hada simintin.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG