Har Yanzu Za a Iya Kiyaye Mace-Macen Yara Da Matasa

Mace macen yara da matasa ya ragu tun daga shekarar aluf dari tara da cisi’in da tara, kuma za’a iya kiyaye wasu da yawa da su ke faruwa.

Mr. Theo Vos na jami’ar Washington dake birnin Seattle, ya ce akwai bukatar yin amfani da wasu hanyoyi, ciki harda fadakar wa akan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara, tun da akwai yiwuwar iyaye matan da suka sami fadakarwa za su yi wa ‘yayansu rigakafi ko su nemi duk wata kariya daga sauro.

Mr. Theo ya kuma ce samun nasarar aiwatar da hakan ba kawai sakamakon kiyaye wadannan matsalolin zai haifar ba, amma harda yadda ake kula da mara lafiya.

A kasashen da gwamnatocinsun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya ba su da karfi, abubuwan da ake bukata da za su taimaka su kuma rage cututtuka ba ‘a samarda su, ko kuma sun yi kadan.

Masu nazarin cututtuka a duniya sun yi nazarin alkaluman mace mace da raunuka da aka samu daga kasashe 188 na kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5, da ‘yan shekaru 5 zuwa 9, da kuma ‘yan shakrau 10 zuwa 19.

Jimla duka an sami mace mace miliyan 7.7 a fadin duniya cikin shekarar 2013 kuma fiye da miliyan 6 yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar.

Yawancin dalilan mace-macen sun hada da cututtukan da suka shafi numfashi a kananan yara da, gudawa da kuma hadarin ababen hawa a matasa.

A shekarar 2013, alkaluma sun nuna cewa Najeriya ta sami mace mace fiye da kashi 3 na jimlar, sanadiyar masassarar cizon sauro, haka kuma kasar Indiya ta sami mace macen kashi 3 sakamakon matsalolin da suka shafi rashin isasshiyar iska wajen haihuwa. Najeriya da, Indiya, da Janhuriyar Demokradiyyar Congo da Pakistan da kasar Habasha sun sami rabin kason mace acen da aka samu sanadiyyar cutar gudawa a kananan yara.

Tsabtataccen ruwan sha da Tsabtataccen muhalli, da abinci mai gina jiki, da samun wadatar rigakafin gudawa za su iya taimakawa wajen rage adadin mace-macen, a cewar Mr. Vos.