Ranar litini data gabata ne kanfanin nan mai bada hayar shirye shiryen talabijin da fina finai ta hanyar yanar gizo mai suna iROKO a Najeriya ya bada sanarwar wata sabuwar yarjejeniya da ta kai yawan kudi dalar Amurka miliyan 19, wanda ya hada da babbar tashar talabijin ta Faransa domin fadada ayyukan sa da zasu mamaye daukacin nahiyar Afirka.
Yarjejeniyar ta zo ne bayan wasu 'yan makwanni kadan da kanfanin Netflix ya fitar da sanarwar fadada kasashen da yake bada hayar finafinai zuwa 190, wanda ya hakan ya zamo tamkar wata gasa tsakanin kamfanin da na iROKO mai mazauni a Lagas Najeriya.
Mai kanfanin Jason Njoku ya ce zasu fadada wuraren da zasu rika shirye shiryen Nollywood a cikin nahiyar Afirka, kuma suna shirin fara nuna shirye shiryen ne ta hanyar anfani da harsuna kamar su Farasanci da Swahili, da Zulu da sauran su.
Kamfanin ya bayyana cewa zai kara yawan awoyin da zai rika anfani dasu wajan yada shirye shiryen Nollywood zuwa 300 a cikin shekarar 2016, da kuma niyyar ninka su zuwa shekarar 2018.
Nollywood Dai shine na biyu mafi girma a cikin kamfanonin fina finai a duniya kuma yana taka rawar gani a wajan hada fina finai da kuma tattalin arzikin kasa a Najeriya.