Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba A Majalisa- Abu Ibrahim

Sanata Bukola Saraki, sabon shugaban Majalisar Dattijai, Yuni 9, 2015.

Bayan fiye da watanni biyu da kaddamar da majalisun tarayyar Najeriya, majalisun basu yi zaman da ya kai na makonni uku ba biyo bayan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyar APC mai mulki.

Bayan dinke wannan Baraka ne majalisun suka sake lale wajen maida hankali kan abinda suka ce yana ciwa talakawa tuwo a kwarya. Tare da cin alwashin marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a yunkurinshi na ganin ya cimma burinsa na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasa kasa.

Ko da yake ana ganin an sami masalaha a majalisar ganin yadda aka rika tada jijiyar wuya da kuma ba hammata iska a farkon tafiyar majalisar, wadansu ‘yan majalisar sunce har yanzu tana kasa tana dabo sai dai kasancewarsu dattawa, zasu ci gaba da kokarin ganin an gyara.

A cikin hira da Muryar Amurka ‘yan majalisa da dama sun bayyana kudurin majalisar na tunkarar matsalolin da suka addabi talakawan kasar, musamman matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya inda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da tada kayar baya.

Wakiliyarmu Madina Dauda na dauke da ci gaban rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Madina Dauda-2:53"