Wannan ya biyo bayan ci gaba da tsanantar aika-aikar ‘yan bindiga dake sace mutane a duk lokacin da suka ga dama al'amarin kuma dake damun tsoffin hafsoshi irinsu Group Captain Sadique Garba Shehu mai murabus.
Captain Shehu yace wannan yanki shine sansanin kusan dukkan sojojin Najeriya amma ace yan bindigar na cin karensu ba babbaka, yace kamata yayi ace wannan wuri shine yafi ko ina tsaro da aminci amma kuma sai aka sami akasi.
Kodayake kwamishinan harkokin tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan yace basu cika son magana kan irin matakan da suke dauka ba, amma dai suna daukar matakan yiwa tufkar hanci don samawa jama'a tsaro.
Karin bayani akan: jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ‘yan bindiga, Boko Haram, sojojin, Nigeria, da Najeriya.
Shima Manjo Janar Yakubu Usman na mai cewa ai reni nema ga sojojin ace ‘yan ta'adda suje har kusa da manyan cibiyoyin tsaro suna tafka aika aika.
Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba yace daga watan Aprilun da ya gabata zuwa watan Mayu sama da manya manyan ‘yan bindiga dari shida suka kama a sassa daban daban na kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5