Magajin Garin birnin New York Bill de Blasio yace yakamata mutane su saurara su samu cikkakken bayani game da tsahin wani bam a daren Asabar a unguwar Manhattan wanda yayi raunata mutane 29.
WASHINGTON, DC —
Wani jami’in tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa bincike da ake gudanarwa bai bada muhimmanci ga masu ikirarin daukar alhaki da aka dora a kan shafin zumunta na Tumbler a ranar Lahadi.
Tuni dai Tumbler ta janye wannan labarin daga kan shafinta na duniyar gizo kuma bata ce uffan ba a kan batun.
Gwamnan jihar New York Andrew Cuomo yace wannan pashewar aiki ne na ta’addanci, sai dai yace babu wata shaida da ta nuna akwai hannun yan kasar waje.
Cuomo yacce akwai Karin yan sandu dubu guda da za’a tura su rinka sintiri a cikin tashohin jiragen kasa na birnina matsayin wani mataki na rigakafi.