Wata kotun daukaka karar kasar Sweden ta yi na’am da warantin kama wanda ya kirkiro WikiLeaks Julian Assange bisa zargin yiwa wata mace fyade. Hukuncin da kotun ta yanke ya share fagen a yiwa Mr Assange tambayoyi a London a watan gobe idan Allah ya kaimu
Mr Assange ya sha musunta zargin cewa ya yiwa wata mace fyade a shekara ta dubu biyu da goma, kuma ya sha kokarin ganin anyi watsi da wannan batu, to amma hakarsa bata cimma ruwa ba.
Yau Juma’a kotun daukaka kara a Sweden tace tayi na’am da nazarin da wata kotun gunduma tayi cewa ana tsamani ko kuma ana zargin Julian Assange da yiwa wata mace fyade
Tun shekara ta dubu biyu da goma sha biyu lokacinda gwamnatin Ecaudor ta bashi mafakar siyasa, Julian Assange yake zaune a ofishin jakadancin Ecuador a birnin London.
Yace yana tsoron zuwa kasar Sweden, domin yana zaton gwamnatin kasar Sweden za ta iza keyarsa zuwa nan Amirka, inda akwai yiwuwar ayi masa shari’a bisa caje cajen cin amanar kasa a saboda rawar daya taka wajen bayyana takardun gwamnati na sirri.