Wani babban jami’in leken asirin Amurka ya fada a jiya Talata cewa shugaba Donald Trump bai bashi takamaiman umarnin daukar mataki a kan yiwuwar katsalandar da Rasha zata yi a zabukan yan majalisu a cikin wannan shekarar 2018 ba, ganin yadda Moscow din ta aikata a zaben shugaban kasa a shekarar 2016 da zummar taimakawa Trump ya lashe zaben.
Darektan Hukumar Leken Asirin na'urori da kuma hukumar Kare muradun yanar gizo na Amurka, Admiral Mike Rogers, ya fadawa wakilan majalisar dattawa cewa ba a ba shi wani umarnin na daukar karin matakin da ya wuce irin ikon da yake da shi a yanzu ba.
Yace ya dauki matakan da suke a karkashin irin ikonsa, yana kokarin toshe duk wata kafar da za a iya amfani da ita don cutar da Amurka, inji Rogers a lokacin da yake bada bahasi ga kwamitin ayyukan soji na majalisar dattawa. Yace ba a bashi wani karin iko ba.
Rogers yace yayi imani shugaban Rasha Vladmir Putin ya dauka a ransa cewa babu wani mummunan sakamakon da zai iya fuskanta don yayi katsalanda a zaben Amurka, a saboda haka zai ci gaba da irin wannan katsalanda. Admiral Rogers yace, ba mu dauki matakan da suka wadatar wajen takalar wannan batu ba.