Har Yanzu babu Labarin Jami'an MDD Da Aka Sace Congo

Wasu mambobi biyu na wata kotun musamman ta MDD da ke duba batun Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wadanda aka sace su ranar Lahadi har yanzu ba a san inda su ke ba, abin da Ministan Sadarwar Kasar Congo Lambert Mende, ya gaya ma gidan Rediyon Muryar Amurka kenan.

Wata takardar bayanin da gwamnatin ta Congo ta fitar ta nuna cewa Michael Sharp, wanda ba-Amurke ne da Zahida Katalin, wadda 'yar kasar Swedin ce, da kuma wasu 'yan asalin kasar ta Congo su hudu, a cewar takardar, "sun fada hannun wasu masu bakar aniya wadanda har yanzu ba a fayyace ba" a lardin Kasai ta tsakiya. Jami'an tsaro na kan aiki tare da hadin giwar sojojin samar da zaman lafiya na MDD a Congo, don kubutar da mutanen," a cewar takardar.

Da daren jiya Litini, Mende ya gaya ma gidan Rediyon Muryar Amurka cewa jami'an tsaron Congo da na MDD sun shafe tsawon ranar su na neman mutane shidan ta wajen amfani da jiragen sama masu saukar ungulu ba tare da sun gano su ba. Ya ba da tabbacin cewa za a cigaba da nemo mutanen da jirgin sama tun daga safiyar yau dinnan Talata.