Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Kabari Cike Da Gawarwaki a Samaliland


kasusuwan mutum
kasusuwan mutum

Tawagar Masu bincike ta fannin kimiyya sunyi anfani da shebur domin kwashe kasar da aka rufe kabarin da aka binne mutane da yawa a garin Barbera dake Somaliland.

Zurfin ramin da suka tone zai kai tsawon mita 2, inda aka binne mutane 17 wadanda akayi imanin cewa anyi musu kisan gilla ne kana aka binne su a wannan wuri yau kusan shekaru 30 kenan.

Su dai wadannan mutanen ‘yan kabilar Isaaq ne, ana tuhumar cewa sojojin dake biyayya ga mai mulkin kama karyan nan ne Siad Bare suka hallaka su lokacin da suke fada da ‘yan tawaye daga Somaliland a wannan lokacin.

Yau sama da shekaru 25 kenan da aka kawo karshen wannan fadan, kuma Somalind ta ayyana yancin ta daga kasar Somalia, yanzu haka masu bincike na kimiyya suna ci gaba da binciken kaburburan da aka binne mutanen da aka yi wa kisan kare dangi a kasar.

Yanzu dai sama da shekaru biyar da suka gabata kwamitin binciken yaki da hadin kan masu kimiyya ta kasa da kasa suna ci gaba da tono gawarwakin mutanen da aka kashe a wannan lokacin.

Ana haka ne da zummar samar da wadatattun hujjojin da za a iya anfani dasu wajen gurfanad da wadanda suka aikata laifin yaki domin hukuncin da ya dace dasu.

Shugaban wannan kwamitin Khadar Ahmed yace sake tono wadannan gawarwakin wata martaba ce ga wadanda aka turbude cikin wannan ramin domin ko anyi haka ne ba tare da kowace irin karramawar da ya kamata ayi wa gawa ba.

Yace kowane dan adam yana da damar a binne shi dai-dai yadda addinin sa ya tanada, yace don haka muna sake tono wadannan gawarwakin muna binne su daban-daban sabanin yadda aka jibga su wuri guda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG