Gwamnatin jihar Yobe ta ce har yanzu ba ta gama tantance yawan adadin ‘yan matan da suka bace sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai musu a daren ranar Litinin ba.
Kwamishinan ma’aikatar ilimi na jihar Yobe, Alhaji Mohammed Aminu, ya ce adadi ko kuma kididdiga da jama’a ke bayarwa ba sahihi bane domin har yanzu basu gama tantance adadin ‘daliban da suka bace ba.
A kwai wasu bayanai da ke nuni da cewa ana da ‘dalibai 704 a makarantar, yayin da yanzu haka aka samu 610 wanda hakan ke nuni da cewa ba a san inda sauran 94 suke ba. Sai dai Kwamishinan yace wannan kididdiga bata fito daga hukuma ba.
A cewar Usman Dangote Karasuwa, wani ‘dan jihar Yobe yace yanzu haka suna cikin jimami musamman ma su da suke garin Karasuwa.
A daren ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai farmaki a kan makarantar sakandaren mata ta garin Dapchi dake Jihar Yobe.
Inda rahotanni ke cewa ‘yan bindigar sunyi awon gaba da ‘yan mata 94, amma gwamnati ta musanta wannan kididdiga kasancewar har yanzu ba a kammala tantance yawan ‘daliban da aka rasa ba.
Lamarin garkuwa ko kuma satar mutane ya zamanto wani sabon abu a arewacin Najeriya, ganin yadda a shekarun baya da suka gabata sai dai aji labarin afkuwar hakan a wasu wararen.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5