Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta ce tana kan wayar wa da jama’a kai kan muhimmancin zaman lafiya, biyo bayan kashe-kashen da a kwanakin baya suka auku a jihohin Benue da Nasarawa, ya kuma yi sanadiyar al’umma da dama kauracewa muhallansu.
Majalisar ta ce ta damu matuka da lamarin, inda har ta gabatar da kudurin yayata zaman lafiya don ci gaban kasa.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar, Umaru Tanko Tunga, ya ce sun lura gwamnatin jihar na kashe makudan kudade wajen taimaka wa ‘yan gudun hijira don al’umma su zauna lafiya.
Shi kuma ‘dan Majalisar mai wakiltar Doma ta Kudu, Dangana Akoza James, ya ce rikicin ya haddasa mummunan koma baya a yankinsa kasancewar suna makwabtaka da jihar Benue.
A halin da ake ciki kuma, rahotanni na nuni da cewa ‘yan sanda sun cafke wasu mutane hudu da ake zargi da haddasa kisan mutane 73 a ranar 1 ga watan Janairu a jihar Benue.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum