Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Tunawa Da Harshen Uwa Ta Majalisar Dinkin Duniya


Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya
Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya

A kokarin ceto harsuna daga mutuwa ko gurbacewa ya sa hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Dinin Duniya ta kebe kowace ranar 21 ta watan Fabrairu a matsayin ranar tunawa da harshen uwa a duk fadin duniya.

Kidigdigar hukumar dake kula da al'adu da ilimi ko UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta nuna cewa kashi hudu cikin dari na harsunan duniya dubu bakwai ne ake anfani dasu wajen koyaswa a makarantu.

Rashin yin anfani da harshen uwa wajen ba da ilimi na yiwa bil Adama barazana saboda harsuna na saurin bacewa ko kuma su gauraye da wasu har su mutu.

Farfesa Haliru Anfani na Jami'ar Usumanu Dan Fodio dake Sokoto ya bayyana mahimmancin wannan ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe. Ya ce an zauna an ga irin mahimmancin da harshe yake dashi. Injishi, harshe shi ne mutum. Dalili ke nan da Majalisar Dinkin Duniya ta hukumarta,UNESCO ta ga ya zama wajibi mutane su koyi harsunansu. Dalili ke nan ranar 21 ta kowane watan Fabrairu ta zama ranar tunawa da harshen uwa.

Kawo yanzu akwai kokarin da gwamnatoci daban daban su keyi domin bunkasa harshen uwa a kasashensu.

Shi ma Farfesa Yakubu Azare na Jami'ar Bayero dake Kano ya kara jaddada mahimmancin harshen uwa ga bil Adama. Injishi, yadda harsuna suke mutuwa ko suke lalacewa na da alaka da yadda mutane suka rikesu. Idan suka yi masu rikon sakainar kashi bisa ga kowane dalili zasu yi asarar harsunansu. A cewarsa harshen uwa na da mahimmanci sosai. Yakamata a ci gaba da anfani dashi a kuma rayashi. Idan ba'a magana da harshe yana samun rauni. Amma harshe ya na bunkasa ne yayinda ake nazarinsa ana rubuce-rubuce dashi. Iyaye su koyawa 'ya'yansu harshensu su kuma 'ya'yan su koyawa nasu 'ya'yan.

A saurari rahoton Babangida Jibrin domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG