Har Yanzu Ba’a Iya Tantance Adadin Daliban Kwalejin Yauri Da Suka Rage A Hannun ‘Yan Bindiga Ba

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu (Facebook/Gwamnatin Kebbi)

Duk da cewa an kubutar da wasu dalibai 30 da malami guda da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kwalejin Birnin Yauri na jihar Kebbi watanni shida da suka gabata, ba’a iya tantance adadin daliban da suka rage a hannun 'yan bindigar ba.

Dalibai 30 da aka sace na kwalejin gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi da wani malaminsu sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar ne bayan shafe watanni shida a hannunsu.

Mai baiwa gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi shawara kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki ne ya tabbatar da cewa an kubutar da daliban 30 da malami daya a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Haka kuma mai magana da yawun gwamna Bagudu ya ce za’a duba lafiyar wadanda aka sako kafin a mika su ga iyalansu.

Mutanen arewa maso yamma da tsakiya dai na ci gaba da zama cikin fargaba sakamakon hare-haren yan bindigar da gwamnati ta ayyana a matsayin yan ta’adda a baya-bayan nan, duk da kokarin da hukumomin tsaron kasar ke cewa suna yi na tabbatar da kawo karshen miyagun iri a kasar.

A ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021 ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da dalibai da malamai a kwalejin na Birnin Yauri, wadanda har yanzu ba'a iya tantance adadinsu ba, lamarin da ya kai ga mutuwar wani dan sanda.

Bayan makonni biyu da sace daliban, yan bindigar sun sako biyu daga cikinsu, kuma a lokacin ba’a bayyana ko an biya wani kudin fansa ba kafin aka sako daliban biyu.

Sarki ya yi godiya ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan jajircewa wajen tabbatar da ganin an kubutar da daliban.

Dubban mutane ne yan bindiga suka kashe da kuma yi garkuwa da su a jihar Kebbi da wasu jihohin arewa maso yamma a bara, lamarin da ya sa masana tsaro ke yin kira ga gwamnnati ta sauya salon yaki da batagarin.