Kusan wata guda bayan da ‘yan Najeriya suka fara fama da karancin man fetur a kasar, har yanzu alamu na nuni da cewa lamarin na iya kara ta’azzara saboda yadda farashin mai ya tashi zuwa sama da Naira 300 a wasu gidajen mai da ke fadin kasar.
Masu ababen hawa na haya a birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa gidajen mai musamman na ‘yan kasuwa masu zaman kansu na sayar da kowacce litar mai a kan fiye da farashin da aka kayyade na naira 165 inda ake sayarwa naira 300 a wasu gidajen man.
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya bayyana cewa zai shigo da mai lita biliyan 2 da dubu 300 zuwa karshen watan nan na Fabrairu don karawa kan lita biliyan daya da ake da shi a matsayin wani bangare na matakan magance karancin man fetur.
To sai dai kuma masu ababen hawa musamman na kasuwanci na cewa galibin ‘yan kasuwar man musamman masu zaman kan su da ba na kamfanin NNPC ba suna kara kudi kan farashin kowacce lita a Abuja.
Daya daga cikin direbobin tasi a Abuja wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce yana gidan mai kan layi kusan sa’o’i 24 bai koma gida ba don ba ko digon mai a motarsa.
Rahotanni sun yi nuni da cewa wasu gidajen man da suka biya kudin kayayyakin da za’a kawo musu tun watan Disamban bara basu sami mai ba har yanzu sakamakon yanayin karancin da ake ciki.
A yayin da ake ganin layukan sun ragu a makon jiya, lamarin ya kara tabarbarewa tun daga ranar Juma’a, domin gidajen mai da dama sun kasance a rufe, yayin da wadanda ake budewa da sayar da su kan farashi, suna da dogayen layukan masu ababen hawa da ke jira.
A yankin Maitama na birnin Abuja akwai sama da ababen hawa 100 kan layin gidan man dake kusa da otel din Transcorp inda ba’a fara sayar da man ba da misalin karfe 9 na safiyar yau Litinin.
Akasarin gidajen man da ke tsakiya da kewayen birnin Abuja sun kasance a rufe a yayin da kalilan da ke bude, su ke fama da dogayen layuka, ana ta cece-kuce a kan wadanda ke kayyade adadan kudin da za su sayar wa masu mota kan kudi mafi yawa na dubu biyar kacal.
Duk da karancin man da ake fama da shi, ‘yan bunburutu sun mamaye lungu da sakon birnin Abuja da jarkoki suna sayarda jarkoki masu lita 10-12 kan naira dubu 4 da 500 zuwa sama.
Da muka tuntubi wani dan bunburutu a unguwar Asokoro kusa da shelkwatar rundunar ‘yan sanda da bai ambaci sunansa ba, cewa ya yi daga unguwar Zuba ake kawo mu su mai kuma dole ake biyan wadanda su ke kawowa kudi mai tsada.
Malam Sahabi Usman ya bayyana takaici kan yanayim tsada da karancin mai da su ke fuskanta ya na mai cewa ana fama da rashin mai a gidajen mai amma sai ga ‘yan bunburutu kowanne lungu da mai a jarka.
Ya bayyana bukatar gwamnati ta dauki matakan da suka dace cikin gaggawa don talakawa ne ke shan wahala a yanzu.
Wata mai sayarda abinci a layin AYA malama Rabi, ta ce matsalar karancin man fetur ta shafi farashin kayayyakin abinci a kasuwa kuma hakan na neman durkusar da sana’arsu.
A jihar Legas kuma gidajen man fetur na 'yan kasuwa masu zaman kan su na sayar da kowacce litar mai a kan sama da naira 200, a jihar Adamawa ma rahotanni sun yi nuni da cewa ana sayar da man a kan samaa da 250 a tsakiyar fadar gwamnatin jihar da dai sauransu.