Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Ba Da Jimawa Ba Za’a Ga Karshen Wahalan Karancin Man Fetur Da Ake Fuskanta A Najeriya - NNPC


Malam Mele Kyari
Malam Mele Kyari

A daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantan karancin man fetur a kusa fadin kasar, kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya jadada cewa ba da gangan aka shigo da gurbataccen man fetur mai cike da sinadarin Methanol mai yawan gaske cikin kasar ba.

Kamfanin dai ya kara jadada cewa, babu yadda za a yi masu shigo da man fetur din su san da cewa man na dauke da sinadarin methanol, domin duba sinadarin na methanol baya da cikin aikin tantance man da ake shigowa da shi cikin kasar a matakin farko da ake bukata ga hukumomin da abin ya shafa ba saboda kaso 1 cikin 100 na sinadarin ne ke cikin kayadadden tsarin tace mai da kasar ta shiga da kamfanonin shigowa da man cikin kasa.

Shugaban kamfanin na NNPC, Mal. Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken al’amuran da suka shafi shigo da gurbataccen mai cikin kasar.

Mal. Kyari ya ce babu yadda za a yi kamfanin NNPC da saura hukumomin kula da harkokin shiga da man fetur cikin kasar zasu gano wannan sinadarin methanol su yi shiru idan ba dai kamfanoni masu samar da maan suka sanar da su ba duba da yadda duba sinadarin methanol baya cikin bukatun su a tsarin samar da man.

Kyari ya bayyana cewa tashar lodin man daga inda aka shigo da su cikin Najeriya ya dade yana samar da man fetur, domin shi ne babbar tashar da ke samar da mai ba ga kasashen yammacin nahiyar Afirka har ma da kasashe da dama na Turai.

Shugaban na NNPC ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan da karshen watan Febrairu kamfanin zai kammala aikin kai kimanin litar mai biliyan 2 da dubu 100 cikin tsarin fadin kasar don kawo karshen wahalan mai da yan kasa ke fuskanta.

Mal. Kyari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kamfanin NNPC na daukan dukkan matakan da suka dace don ganin ya ci gaba da samar da wadataccen mai da ake bukata a cikin kasar, kuma kamfanin na da ingantaccen tsarin samar da adadin man da 'yan kasa ke bukata na yau da kullum.

Mal. Kyari ya bayyana ne a gaban ‘yan majalisar a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan karancin man fetur da ke kara ta’azzara musamman a birane Abuja, Legas, da kuma wasu sassan kasar inda daruruwan masu ababen hawa suka makale a kan dogayen layukan da ake yi a gidajen mai a sassa daban-daban na kasar.

Haka kuma, a wani bangare na matakan shawo kan lamarin, kamfanin ya umurci dukkan ma'aikatunsa da depo-depo da su fara aiki na sa'o'i 24 a fadin kasar don rage wahalhalun da yan kasa ke fuskanta a yanzu.

Ko a ranar talata ma sai da babban daraktan sashen kamfanin dake kula da sarrafa tare da rarraba man fetur a kasar, Adetunji Adeyemi, ya bayyana cewa tuni kamfanin ya kara habaka aikin rabon mai a fadin kasar kuma ya kafa tawagar sa ido tare da goyon bayan hukuma da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da rarraba man fetur cikin sauki a fadin kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG