Shugaban ya yi bayani ne akan yadda gubataccen man ya shiga wasu gidajen mai a kasar wanda ya sanya al'umma cikin fargaba da karanci a samun man fetur don gudanar da ayyukansu na sufuri na yau da kullum.
A wata hira ta musamman da shugaban na ma'aikatar dokokin man fetur, Faruk Ahmed, ya bayyana akasin da aka samu a matsayin ya zo ba'a zata sakamakon yadda aka kwashe sama da shekaru 30 ba'a fuskanci irin wannan yanayi ba.
Ma'ikatar dokokin man fetur din dai ta ce zata dauki matakan da suka dace a kan kamfanin da aka yi yarjejeniyar shigowa da man fetur din cikin Najeriya da shi sakamakon yadda ta gano kamfanin da ya aikata hakan bayan bincike mai zurfi.
Kamfanin da aka gano ya shigo da gurbataccen man wanda ke da sinadarin Mathanol da ya wuce kima dai ya shigo da jiragen ruwa na man da ya kunshi tan dubu 30 ne kan tekun kasar wanda da zarar aka gano, ma'aikatar dokokin man fetur din ta maida jirage 3 cikin hudu kasar da ta shigo wa Najeriya da su.
Shi ma kamfanin NNPC zai dauki matakan da ya dace kan wannan batu kamar yadda Malam Faruk Ahmed ya bayyana.
Saurari yadda hirar tasu da Halima AbdulRa’uf takasance cikin sauti: