Yanzu haka dai takunkumin da kungiyar ECOWAS din ta kakabawa Jamhuriyar Nijar na ci gaba da haifar da mummunan tasiri kan harkokin kasuwanci da sauran al’amuran tattalin arzikin kasar.
A watan Yulin da ya gabata ne sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Mohammed Bazoum tare da tsare shi da iyalansa.
A wani taro na baya bayan nan da shugabannin Kungiyar ECOWAS suka gudanar a Abuja, sun gindaya wa mahukuntan Nijar din wasu sharuda kafin a dage wadannan takunkumai na karya tattalin arziki.
Sharudan sun hada da gaggauta sakin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa da ma dukkan mutanen da aka kama a sakamakon wannan al’amari, kafin a fara duba hanyoyin dage takunkumin da ka kakaba wa kasar.
A hirar su da wakilin mu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari, Ambasada Bala Sani, tsohon Jakadan Najeriya a kasashen Jamus, Mouritaniya da kuma Ghana ya fayyace wasu daga cikin hanyoyin diflomasiyya da ka iya warware takaddamar.
Saurari cikakkiyar hira cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5