WASHINGTON, D. C. - Daruruwan magoya bayan juyin mulkin ne suka taru a gaban majalisar dokokin kasar da ke Yamai babban birnin kasar, inda suke ta kade-kade na nuna goyon bayan sojojin yayin da aka kwarara ruwan sama da sanyin safiya.
Wasu daga cikinsu sun daga tutocin kasar Rasha tare da rera taken nuna kyama ga Faransa, da kuma nuna rashin jin dadinsu ga tsohuwar mulkin mallaka na Faransa da kuma tasirinta a yankin Sahel.
Rundunar sojin, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban hafsan hafsoshinta, ta ce ta yanke shawarar yin aiki da sanarwar da sojoji suka yi, a wani jawabi da suka yi a cikin daren da ya gabata ta gidan talabijin na cewa sun tube shugaba Mohamed Bazoum daga mulki.
Sojoji na bukatar "kare lafiyar" shugaban kasar da iyalansa da kuma guje wa "mummunan fada, da zai iya haifar da zubar da jini da kuma shafar tsaron jama'a," in ji ta.
Dakaru a Mali da Burkina Faso sun kara kusantar Rasha tun bayan da suka karbi ragamar mulki, a shekarar 2020 da 2022, tare da yanke alaka da kawayen kasashen yamma na gargajiya.
A ranar Laraba ne dai aka fara karbar ragamar mulki, yayin da wasu masu gadi a fadar shugaban kasar da ke Yamai suka rufe shi, inda suka tsare shugaban a ciki.
Wani jami’in rundunar sojin sama mai suna Kanar Amadou Abdramane ne ya karanta sanarwar da aka watsa ta gidan talabijin a daren ranar Laraba, wanda kuma ya bayyana a ranar Alhamis cewa an dakatar da duk wasu harkokin jam’iyyun siyasa har sai an sanar da su.
Bazoum, a wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta ta Twitter a safiyar ranar Alhamis, ya sha alwashin kare tsarin mulkin dimokiradiyya da aka sha wahala wajen kafawa.