Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Sudan Ya Shiga Wata Na Biyu Yayin Da A Ke Ci Gaba Da Gwabza Fada


Ricikin Sudan.
Ricikin Sudan.

Sojojin Sudan sun kai wani hari ta sama a arewacin Khartoum babban birnin kasar a ranar Litinin, kan abokan gaba da ke kusa da wani asibiti da wasu shaidu suka ce an samu barna a harin.

An gwabza kazamin fada a birnin Khartoum da sauran biranen Bahri da Omdurman, duk kuwa da tattaunawar da Saudiyya da Amurka suka samar tsakanin sojojin kasar da dakarun sa kai na RSF a birnin Jeddah da nufin samar da hanyoyin jin kai da kuma tsagaita wuta.

Fadan dai ya bazu zuwa yammacin yankin Darfur, amma ya fi karkata ne a babban birnin kasar, inda mayakan RSF suka mamaye unguwanni, kuma sojojin sun yi amfani da hare-hare ta sama da manyan bindigogi wajen kai musu hari.

A cikin wani sakon sautin murya da kungiyar ta RSF ta fitar, shugabanta Mohamed Hamdan Dagalo, ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa an kashe shi ko kuma an jikkata shi a yakin.

Hafsan sojojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da Dagalo sun rike manyan mukamai a majalisar mulkin Sudan, bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekara ta 2019, a lokacin boren al'ummar kasar, kuma suka yi juyin mulki shekaru biyu bayan da wa'adin mika mulki ga farar hula ya gabato.

An fara fadan ne a watan da ya gabata bayan takaddama kan shirin kungiyar RSF na shiga aikin soja, da kuma tsarin shugabanci a wani sabon sauyin siyasa.

Hakan dai ya sa kusan mutane 200,000 suka yi gudun hijira zuwa kasashen da ke kusa da kuma wasu fiye da 700,000 da suka rasa matsugunansu a cikin kasar Sudan, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Wadanda har yanzu ke cikin birnin Khartoum na cikin zulumi da neman hanyar samun tsira.

XS
SM
MD
LG